IQNA

Mahajjata Suna Gudanar Da Jifar Shaidan Jamratul Aqbah

23:32 - September 01, 2017
Lambar Labari: 3481854
Bangaren kasa da kasa, Tun da jijjifin safiyar yau ne mahajjata kimanin miliyan biyu suka fara gudanar da jifar shaidan a ranar idin layya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Rahotanni sun ce tun da jijjifin safiyar yau ne mahajjatan suka fara isa wurin jifar jamratul Aqbah, inda kimanin mahajjata miliyan biyu ne suke gudanar da wannan aikin ibda a bana.

Mahukuntan kasar saudiyya sun ce sun dauki dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da kuma tsaria yayin gudanar da jifan Shaidan.

Inda bayanin ya ce an saka na'urorin daukar hoto guda 500 a wurin, domin duba yadda komai yake gudana a wurin, da nufin ganin an kauce wa matsalar da aka samu ta tirmutsitsi a shekaru biyu da suka gabata, inda mutane fiye da dubu 7 suka rasa rayukansu.

3636937


captcha