IQNA

Ganawar Sadat A Kasar Austria A Ranar Ghadir

21:28 - September 07, 2017
Lambar Labari: 3481872
Bangaren kasa da kasa, mata masu alaka da sadat suna gudanar da wata ganawa a ranar idin Ghadir a cibiyar cibiyar Imam Ali (AS) da k birnin Vienna na kasar Austria.

Kamfanin dllancin labaran iqna ya habata cewa, ya nakalto daga shafin telegram na cibiyar Imam Ali (AS) cewa, kamar yadda aka saba mata sadat suna gudanar da wata ganawa a ranar idin Ghadir a cibiyar cibiyar Imam Ali (AS) da k birnin Vienna domin yin taron ranar.

A ranar wannan Asbar mai zwa idan Alah ya kai mu ne za a gudanar da tarukan ranar idil Ghadir a dukkanin kasashen kasashen duniya, kuma wannan cibiya za ta gudanar da taro domin yin murnar da zagayowar wannan rana mai daraja da albarka da matsayi na musamman a cikin addinin muslunci.

Cibiyar musulmin birnin Vienna ta isar da sakon taya murnar Ghadir ga dukkanin al’ummar musulmi na duniya, musamman mabiya tafarin iyalan gidan manzon Allah.

3639241


captcha