IQNA

UN: Adadin Musulmin Rohingya Da Aka Kashe Ya Haura Dubu

22:58 - September 08, 2017
Lambar Labari: 3481876
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta ce adadin musulmi ‘yan kabilar Rohingya da aka kasha a kasar Myanmar ya haura dubu daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wasu alkalumma dake cewa yawan musulmi 'yan Rohingya da suka rasa rayukansu a hare-haren da sojojin kasar Myanmar suke kai masu ya haura dubu guda.

Da take bayyana hakan mai tattara bayanai ta musamen ta MDD a kasar ta Myammar,Yanghee Lee, ta ce adadin 'yan Rohingya da suka mutu a yankin Rakhine dake arewa masi yammacin kasar zai iya wuce dubu guda.

Wannan adadin dai ya linka sau biyu alkalumen da gwamnatin Myammar din ta sanar a baya.

Jami'ar ta kara da cewa an samu rasa raykan daga bangare biyu, aman mafi yawan wadanda suka mutu muslmin Rohingya ne, sannan ta kara da cewa babban abun bakin ciki shi ne ba suda ikon shiga yankin domin ganin abunda ke faruwa, amman ta ce wannan lamari zai iya kasance mafi muni da duniya da kasar ta Myammar ta gani a 'yan shekarun baya baya nan.

3639730


captcha