IQNA

21:23 - September 15, 2017
Lambar Labari: 3481899
Bangaren kasa da kasa, jami’an ‘yan sanda na birnin London sun ce tarwatsewar wasu ababe a cikin tashar jirgin kasa da ke birnin harin ta’addanci ne.

Kamfanin dillancin labara ina ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na alalam cewa, jami’an ‘yan sanda na birnin London sun ce tarwatsewar wasu ababe a cikin tashar jirgin kasa da ke birnin yana a matsayin harin ta’addanci kuma ana kiraga sauran jama’a duk wada ya samu wani bayani da ya sanar da ‘yan sanda.

A yau ne wani abu ya tarwatse bayan da aka ajiye wata leda da take dauk da wasu abubuwa da ba a sani ba a ckin wani tarragon jirgin kaa a tashar jiragen kasa da ke birnin London, inda mutan suka samu raunuka.

Wanan dai bas hi n karon farko da ake kai harin ta’addanci a birnin London ba, kamar yadda hatta wanna tasha ta fuskanci irin wadannan ayuka a lokutan baya.

Sakamakona bin da ya faru, jami’an tsaro sun sanar da cewa sun rufe wannan tasha har zuwa wani lokaci a nan gaba, bayan sun kammala gdana da bincike kan batun.

3642106


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: