IQNA

Mahukuntan Bahrain Sun Hana Saka Alamun Ashura A Kuruzkan

22:02 - September 19, 2017
Lambar Labari: 3481912
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan masarautar kama karya ta kasa Bahrain sun dauki mataki hana hana gudanar da duk wani taro mai alaka da Ashura.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daidai lokacn da ake shirin fara gudanar da tarukan Ashura a dukkanin fadin duniya, mahuntan mulkin kama karya na kasar Bahrain sun tura jami’an tsaro domin kwace duk wata alama ta Ashura a garin Kuruzkan.

Wannan ya zo ne ‘yan kwanaki bayan wani farmai makamancin haka a garuruwan Satra da Nudarat.

Mahukuntan masaratar kama karya ta Bahrain sun jima suna hankoron ganin sun hana gudanar ta tarukan ashura da ma duk wasu taruka da ska shafi mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah, wadanda su e suka fi yawa a kasar.

Yanzu haka dai suna kwace kayyalaye da tutocin da suke dauke da snan Imam Hussain (AS) a duk inda suka gan su.

3643984


captcha