IQNA

Shirye-Shiryen Kwanaki 10 Na Muharram A Birtaniya

23:45 - September 21, 2017
Lambar Labari: 3481918
Bangaren kasa da kasa, a gobe ne za a fara gudana da tarukan kwanaki goma na watan muharram a babbar cibyar musulunci ta Birtaniya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, cbiyar musluncin ta bayar da sanarwar cewa, daga gobe za a fara taruka kamar yadda aka saba daga farkon watan Muharram.

Zaman na farko na gobe za a gudanar da jawabai ne a ginin cibiyar a cikin harshen farisanci, inda sheikh Ahmad Waizi da kuma sayyid Hashim Musawi za su gabatar da jawabai ga mahalarta taron.

Kamar yadda shi ma hajiBehzad maulayi zai gabatar da wakoki kan wannan wakia mai girma.

Haka nan kuma da dare da kimanin karfe 19:45 za a gudaar da wani taron wanda inda za a yi bayanai a cikin harshen turanci, wanda kowa zai iya halarta.

Wadannan taruka dai za su ci gaba har zuwa ranar goma ga watan muharram ranar da ake gudanar da tarukan na ashura, inda za a kammala tarukan da bayanai na karshe.

3644758


captcha