IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi ta Yi Allah Wadai Da Harin Las Vegas

23:37 - October 03, 2017
Lambar Labari: 3481964
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakakusar suka dangane da harin da aka kaddamar a birnin las Vegas na Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren kungiyar kasashen musulmi Yusuf Usaimin ya bayyana cewa, harin da aka kai a birnin la Vegas bababn abin takaici ne.

Ya ci gaba da cewa wanann harin aiki ne na dabbanci kuma yana nuna rashin imanin mustumin da ya kai harin tare da bayyana alhini ga iyalan wadanda suka rasa raykansu sakamakon harin.

Shi dai ba'amurken dan shekaru sattin da hudu a duniya ya hallaka mutane sama da hamsin tare da raunana wasu daririwa a ruwan harsashen da ya yitun daga hawana talatin biyu na benen wani otel mai suna, Mandalay Bay Hotel,kan wani dandazon jama'a dake halartar wani filin raye-raye na bainar jama'a.

Tun da farko dai bayanaisun ce 'yan sanda sun kashe mutimin, saidai rahotannibaya bayan nan sun ce mutimin ya hallaka kansa ne kafin 'yan sanda su tarda shi.

Wannan dai shi ne harin bindiga mafi muni da aka taba gani a Amurka.

ShugabaAmurka a wani jawabinsa da yammacin nan ya danganta harin da babban abun takaici.

3648535


captcha