IQNA

An Dinka Tuta Mai Tsawon Mita Dubu 4 Domin Mika Ta Ga Hubbaren Imam Hussain (AS)

22:27 - October 27, 2017
Lambar Labari: 3482041
Bangaren kasa da kasa, an dinka wata tuta mai tsawon mita dubu 4 a lardin Dayala na ‘yan sunna a Iraki domin mika ta kyauta ga hubbaren Imam Hussain (AS).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alahd cewa, Hassan bawi shi ne shugaban cibiyar da ke kula da wuraren ziyara a lardin Dayala, shi ne kuma ya jagoranci aiki.

Hassan bawi ya ce an kammala aikin dinkin wannan tuta ahalin yanzu, kuma nan da mako mai kamawa za a mika ta ga hubbaren Imam Hussain (AS) da ke Karbala.

Ya kara da cewa, dukkanin bangarori a lardina dayala sun shiga cikin wanann aiki, kuma kamar yadda aka sani mafi yawan mutanen lardin Dayala ‘yan snna ne, kuma su ne suka kirkiro wannan aiki tare da gayyatar dukkanin bangarori na shi’a da kurdawa da turkaman da sauransu domin a yi aiki tare.

Bawi ya ce wannan lamari yana da babban sako da yake aikewa da shi ga dukkanin al’ummomin musulmi da ma na duniya baki daya, kan cewa al’ummar Iraki al’umma ce guda, kuma duk wanda ya nemi raba kansu ba zai yi nasara ba.

3657159


captcha