IQNA

Shirin Raba Kwafin Kur’anai A Kasashe 15 Na Afirka

22:33 - October 27, 2017
Lambar Labari: 3482043
Bangaren kasa da kasa, cibiyar wakafi ta Mehr a lardin Quniya a kasar Turkiya za ta raba kwafin kur’ani dubu 21 da 500 akasashe 15 na Afirka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Anatoli cewa, wannan cibiya za ta gudanar da wannan aiki ne mai take ‘yan uwanmu a Afirka.

Igol Erdam shugaban wannan cibiya ya bayyana cewa, akwai ayyukan da wannan cibiyar take aiwatarwa awasu kasashe, kma ya zama wajibi ta ayar da hankali ga ‘yan uwa musulmi da suke a nahiyar Afirka.

Daga cikin ayyukan da wannan cibiya take yi akwai gina masallatai da makarantun addini da kuma taimaka ma malaman makarantun kur’ani, gami da samar da kayan koyar da karatu a makarantun musulmi.

Ya ce akwai wasu daga cikin kasashen Afirka wadanda wasu daga cikin makarantun kur’ani na fuskantar matsaloli, wada hakan yasa suke yin amfani da hanyoyi na gargajiya domin koyar da kr’ani a makarantu.

Yanzu haka dai wannan cibiya ta aike da dubban kwafin kur’anai wadanda za afara raba sua cikin wasu kasashen nahiyar da ake fuskantar matsalolin na rashin kur’anai a makarantunsu.

3657138


captcha