IQNA

An Kafa Wuraren Karatun Kur’ani 100 Na Mata A kan hanyoyin Zuwa Ziyarar Arbaeen

23:33 - October 28, 2017
Lambar Labari: 3482047
Bangaren kasa da kasa, an kafa warren karatun kur’ani mai tsarki da ya shafi mata zalla a kan hanyoyin zuwa ziyarar arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da gudanar da shirye-shiryen ziyarar arbaeen, yanzu haka an kafa warren karatun kur’ani mai tsarki da ya shafi mata zalla a kan hanyoyin zuwa wannan ziyara a cikin kasar Iraki.

Bayanin ya ce wadannan wurare an kafa su ne a cikin larduna 12 na kasar Iraki da suke isa hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala.

Baya ga haka kuma akwai shirye-shirye da daman a ilmantarwa da kuma fadakarwa ga masu ziyarar, wanda malamai da masana za su rika jagoranta domin samun faida da kuma ilmantuwa da abubuwa da manzon Allah da kuma ahlul bait suka koyar da al’ummar musulmi.

A nasu bangaren su ma jami’an tsaro sun dauki dukkanin matakan da suka dace domin bayar da kariya ga masu gudanar da wannan ziyara, inda jami’an tsaroa cikin kayan sarki dauki da kayan aiki suka kafa shingaye a kan dukkanin hanyoyin da suke isa cikin garin na Karbala, yayin da wasu kua suke sintiri.

3657298


captcha