Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taron shi ne karo na tara da ake gudanar da shi, inda mataimakin babban limamain kasar Ghana ya kasance a wurin tare da wasu malaman kiristoci.
Sheikh Armayau Shu'aibu shi ne mataimakin babban limamin kasar ta Ghana, a lokacin da yake gabatar da jawabi ya bayyana cewa, gudanar da irin wannan taro yana da muhimmanci domin kara kusanto da fahimta a tsakanin mabiya addinai.
Kamar yadda su ma a nasu bangaren malaman addinin kirista sun bayyana musulmi a matsayin 'yan uwansu, wadanda suke 'yan kasa guda kuma suke rayuwa tare.
Dukkanin bangarorin biyu sun jaddada wajabcin yin aiki tukuru a tsakanin malaman addinai na kiristanci da musulmi wajen wayar da kan mabiyansu kan muhimamncin zaman lafiya da hakuri da juna, da kuma girma juna.