IQNA

Wahabiyanci Ne Ya Jawo Yaduwar Tsatsauran Ra'ayi A Najeriya

16:57 - October 31, 2017
Lambar Labari: 3482053
Bangaren kasa da kasa, wasu masana a Najeriya suna ganin cewa akidar wahabiyanci ce babban dalilin yaduwar tsatsauran ra'ayi da ta'addanci a Najeriya.
Wahabiyanci Ne Ya Jawo Yaduwar Tsatsauran Ra'ayi A NajeriyaKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wasu masana a Najeriya suna ganin cewa akidar wahabiyanci ce babban dalilin yaduwar tsatsauran ra'ayi da ta'addanci da ya addabi Najeriya a halin yanzu.

Bayanin ya ci gaba da cewa, al'ummar najeriya sun kasance masu kaunar juna da girmama raayin juna, amma bayan zuwan akidar wahabiyanci, an fara samun rigingimu a tsakanin musulmi da kafirta juna.

Binciken wanda ya kunshi masana daga sassa na kungoyoyi da kuma masu nazari, ya nuna cewa akidar wahabiyanci ba ta kallon sauran musulmi a matsayin musulmi, matukar dai musulmin ba akan wannan akida suke ba, wanda hakan ne ya sanya yan ta'adda shelanta jihadi kan msuulmi da wand aba musulmi.

Haka nan kuma binciken ya gano cewa dukkanin wadanda suka shiga cikin kungiyar ta'addanci a kasar masu dauke da akidar wahabiyanci ne, kuma suna daukar fatawoyin da suke aiki da su ne da littafan bin taimiya.

Wani abu mai muni kuma shi ne yadda wannan aiki na wahabiyanci ya fara sanya wasu matasa karkata zuwa ga al'adun turaia halin yanzu, saboda suna ganin msuulunci ba addini ne da ya dace da rayuwar dana dam ba.

3658646


captcha