Kamfanin dillancin labaran iqna ya
baya da rahoton cewa, Ibrahim bin Fauzi Akayah karamin yaro ne dan kasar Jordan
wanda ya hardace kur’ani mai tsarki kuma ya karanta ayoyinsa a cikin zama guda
a garin Tufaila na kasar Jordan.
Wannan yaro yana yin karatun nasa ne ta hanyar ambaton farkon kowace aya tun daga farkon kur’ani har zuwa karshe.
Karatun nasa ya bayar da mamaki matuka ta yadda dukkanin malamai da daliban da suk halartar wajen wannan taro suka yi mamakinsa matuka.
Malamai da daman a kur’ani sun bayyana wannan yaro a matsayin abin koyi ga sauran yara wajen karatun kur’ani, ta yadda lakanci kur’ani duk da karancin shekarunsa.