Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa, a jiya babban sakataren kungiyar Hizbullah a Lebanon Sayyid
Hassan Nasrullah ya gana da Ali Akbar wilayati babban mai baiwa jagora shawara
kan batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.
Kafin wann an ganawar Wilayati ya gana da firayi ministan kasar Lebanon saad Hariri, inda a nan suka tattauna akan alaka tsakanin Iran da Lebanon.
Wilayati ya tabbatarwa Hariri da cewa,a Iran a shirye take ta bayar da dukkanin taimako da ya kamata ga kasar Lebanon dukkanin bangarori.
Ali Akbar wilayati dai ya isa kasar Lebanon ne domin halartar babban taron kungiyar hadin kan malaman gwagwarmaya na duniya da aka gudanar karo na biyu a kasar.