Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Aifar Auner 'yar shekaru 66 da haihuwa tana rayuwa ne a garin Buja acikin gundumar Azmir a kasar Turkiya.
Wannan mata ta halarci ajin koyar da karatun kur'ani mai tsarki ne inda a cikin kwanaki 7 kacal ta iya karatun kamar sauran dalibai.
Dukkanin malamai da da daliban wannan makaranta sun yi mamakin yadda wannan mata ta iya karatu a cikin a cikin kwanaki bakawai.
A cikin ain akwai dalibai kimanin 70 wadanda suke koyan karatun kur'ani mai tsarki wadanda sun dauki tsawon lokaci, amma ita mai shekaru ta koyi karatun a cikin mako guda, wanda hakan ya zama abin Makai ga dukkanin mutane, domin kuwa ba a taba ganin hakan ba.