Masar ta kasance a sahun gaba wajen nuna dadaddun kwafin kur'anai a wannan babban baje koli da ke gudana a halin yanzu.
Kur'ani mafi jimawa da aka fi sani da kur'anin Birmingham na daga cikin kwafin kur'anan da ake nunawa a wannan wuri, wanda ake kallonsa a matsayin cikakken kur'ani mafi jimawa ahalin yanzu.
Tun kimanin shekaru biyu da suka gabata ne aka kai wannan kwafin kur'ani a babban dakin ajiyar kayan tarihi na Birmingham da ke kasar Birtaniya.
Tarihin wannan kur'ani na komawa ne zuwa ga lokacin khalifa Usman khalifa na uku, wanda aka rubuta shi a kan jimammayar fata mai karfi.
Wannan baje kolin dai zai gaba daga nan har zuwa makonni biyu tare da halartar jama'a daga ciki da wajen kasar ta hadaddiyar daular larabawa.