Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saumaria News cewa, a
jiya , jami'an tsaron kasar Iraki sun samu nasarar halaka 'yan ta'adda da suke
yunkurin kai harin kunar bakin wake kan masu ziyarar arbaeen a kan hanyarsu ta
zuwa Karbala.
Janar Jalil Ribai shi ne bababn kwanadan ayyukan tabbatar da tsaro da kuma yaki da ta'addanci a Iraki, ya bayyana cewa jami'ansa sun samu nasarar dakile shirin 'yan ta'addan wahabiyyah takfiriyya a lokacin da suke shirin tayar da bam a tsakiyar masu tattakin zuwa Karbala ayankin Ridwaniyya na Iraki.
Jami'an tsaro sun yi kokarin hana mutanen shiga cikin masu tattakin, kafin daga bisani su tarwatsa kansu su biyu, amma babu ko daya daga cikin masu tattakin da ya samu rauni ko rasa rai.
Fiye da jami'an tsaro dubu talatin ne da suka hada da sojoji da 'yan sanda kasar Iraki suke bayar da kariya ga masu gudanar da tattakin zuwa hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin karbala.