Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai brais ya bayar da rahoton cewa, cibiyar kula da bincike da kuma nazari kan addinin muslunci ta da kuma cibiyar bincike mai zaman kanta za su shirya taro a jami'ar Exeter.
Bayanin y ace wanann taro zai mayar da hankali a kan rubuce-rubucen da aka yi dangane da addinin muslunci wanda musulmi suka rubuta, domin tantance hakikanin abin da yake shi ne muslunci da kuma abin da ake rubutawa a kan musulunci.
Daga cikin marubuta na turai akwai masu yin rubutu na batunci a kan addinin muslucni, wanda kuma shi ne akasarin mutanen nahiyar suke karantawa, duk kuwa da cewa akwai rubutun musulmi da dama da ya kamata ya zama ma'auni.
Baya ga haka kuma masana da manazarta da za su halarci taron za su gabatar da mahangarsu kan yadda za a samu daidaiton fahimta, da kuma yin nazari kan yankunan musulmi da tasirin muslunci a sauran yankuna.