IQNA

Wani Musulmi Ya Yafe Wa Wanda Ya Kashe Masa Dansa A Amurka

23:37 - November 11, 2017
Lambar Labari: 3482091
Bangaren kasa da kasa, wani musulmi a birnin Lexington a jahar Kentucky ta Amurka ya yafe wa wani da ya kasha dansabayan an yanke masa hukuncin daurin shekaru 31.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin geo.tv cewa, Abdulmunim Sambat Jitmud ya yafe wa Trey Alexander Relford wani matashi da ya kasha masa yaro a shekara ta 2015.

Wannan lamari ya faru ne a lokacin da matashin yazo domin yin sata a gidansa amma kuma ya kasha masa yaro wanda ya samu a cikin gidan.

Ya bayyana cewa, ya dauki wannan matakin ne domin aiwatar da umarnin muslucni.

Ya kara da cewa, a kowane lokaci addinin muslunci yana yin kira zuwa ga afuwa da yafiya, domin duk lokacin da mutum ya yi yafiya daga lokacin ya bude wani sabon shafin rayuwa.

Dukkanin jama'a sun yi mamakin wannan mataki wanda musulmi suke dauka domin kuwa ya sanya zukatan mutane da dama suna sauya ra'ayinsu kan yadda suke kallon addinin muslucni a matsayin addinin tashin hankali da kisa.

6617993


captcha