Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, fitaccen makarancin kur'ani dan kasar Masar zai yi karatu a wani taron fara maulidin manzon Allah (SAW) a Basarah da ke kasar Iraki a cikin mako mai kamawa.
Wannan taro dai zai gudana ne a masallacin Malak da ke birnin na Basarah wanda babban wakilin Ayatollah Sisatania garin Sheikh Ali Muzaffar zai jagoranta.
A wannan taron Abdulnasir Harak fitaccen makarancin kur'ani dag akasar Masar zai fara budewa da karatun kur'ani da kyakyawan sautinsa.
A lokutan maulidin manzon Allah ana gudanar da tarukan gasar kur'ani da kuma taruka na bayani kan rayuwar ma'aikai, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyakan gidansa.