Wanann yaro dai ya yana yin karatunsa ne bisa salo irin na Mahmud Husri, inda ya samu tarbiya karatun kur'ani a wurin mahaifansa da kuma makarantar da yake zuwa.
Yanzu haka dai yana karatu ne a makarantar firamare a gundumar Manufiyya da ke cikin kasar ta Masar.
Manyan cibiyoyi da suka hada da bababr cibiyar Azahar sun girmama wanann karamin yaro da Allah ya yi masa baiwa ta musamman, da kuma kaifin basira maras misiltuwa, inda lashe gasar hardar kur'ani ta kasa baki daya a Masar, duk kuwa da larurar rashin gani da yake fama da ita.