Bangaren kasa da kasa, Majami'ar kasar Masar ta dakatar da gudanar da tarukan da aka saba gudanarwa na shekara-shekara a kowace ranar hudu ga watan Nuwamba, sakamaon harin ta'addancin da aka kaddamar kan musulmi a masallaci.
Kamfanin
dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A cikin bayanin da majami'ar ta fitar,
Makariyus babban jagoran mabiya addinin kirista na lardin Minya ya tabbatar da
cewa, wannan taro da aka shirya gudanar a babbar majami'ar Minya a yau, an
dakatar da shi, domin nuna alhini ga abin da ya samu musulmi.
Ya ci gaba da cewa hakika harin da aka kaddamar a kan masallaci a lokacin da musulmi suke yin ibada, babban abin tashin hankali ne, domin kuwa hakan ya nuna cewa masu aikata wannan ta'addanci ba su yi imani da wani addini ba.
Ya ce a madadin dukkanin kiristocin kasar Masar, yana isar da sakon ta'aziyya ga dukkanin musulmi na kasar Masar, musamman ma iyalan dukkanin wadanda lamarin ya shafa.
Haka nan kuma ya yi kira ga dukaknin al'ummomin kasar da su hada kai baki daya domin yaki da mummunar akidar ta'addanci.