Kungiyar ta Amnesty International ta yi wannan kiran ne cikin wani sako da ta fitar a shafinta na Twitter inda ta ce sakamaon tabarbarewar yanayin lafiyar Sheikh Isa Qasim, ya zama wajibi mahukutan kasar Bahrain su samar da yanayi na gaggawa da zai ba da dama likitoci su gana da Shehin malamin don yi masa magani.
A shekaran jiya Lahadi ne dai wasu majiyoyi suka bayyana cewar Sheikh Isa Qasim din yana fama da tsananin rashin lafiya sakamakon ci gaba da daurin talalan da gwamnatin Bahrain take masa a gidansa da kuma hana ganawa da shi.
Tun a watan Yunin shekara ta 2016 ne dai gwamnatin Bahrain din ta kwace masa shaidar zamansa dan kasar Bahrain sannan kuma jami'an tsaron kasar suka ci gaba da yin kawanya wa gidansa da hana shi fita lamarin da ke ci gaba da sanya rayuwarsa cikin hatsari.