Wannan taro zai samu halartar bangarori daban-daban na musulmi, inda za a gabatar da jawabai kan muhimamncin hadin kan al'ummar musulmi wanda shi ne babban gishikin nasarar musulmi a cikin lamurransu.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan masallaci zai zama babbar cibiya ta gudanar da tarukan addinin muslunci, da hakan ya hada da sallalo biyar na kowace rana, gami da tarukan addini kamar maulidin amnzon Allah da kuma tunawa da muhimamn ranaku a cikin addinin muslunci.
Wannan dai shi ne karo na farko da mabiya mazhabar shia' suka gina masallacia birnin na Cape Town.