IQNA

Dr. Ali Larijani kakakin Majalisa Jamhuriyar Musulunci:

Tauhidi Da Bin Hakikanin Koyarwar Manzon Allah Su Ne Gishikin Hadin Kan Musulmi.

23:49 - November 30, 2017
Lambar Labari: 3482152
Bangaren kasa da kasa, Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani wanda yake magana a lokacin bukukuwan Mauludin annabi (s.a.w.a) ya yi wa dukkanin al'ummar musulmi murnar zagayowar wannan rana ta haihuwar ma'aikin Allah.

Kamfanin dillancin labara iqna ya ahbarta cewa, Dr. Larijani ya kara da cewa; Idan ace musulmi za su yi aiki da koyarwar da manzon Allah (s.a.w.a) ya zo musu da ita, to da yanayin da musulmi suke ciki a wannan lokacin ya fi haka, ta yadda a yanzu adadinsu ya haura biliyan daya, amma kuma sun rusuna a gaban manyan kasashen duniya.

A nan Iran ana fara bikukuwan Mauludin annabi daga ranar sha biyu ga watan Rabi'ul Auwali zuwa 17 gare shi a matsayin makon hadin kai, kamar yadda Imam Khumaini ya ayyana.

Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya yi ishara da yadda manyan kasashe suke son yin iko akan al'ummar musulmi ta hanyoyi da dama da suka hada da kirkiro kungiyoyin yan ta'adda domin musulmi su rikazubar dajininsu da kansu.

Haka nan kuma Larijani ya yi ishara da irin makircin da makiya addinin muslunci musamamn Amurka da yahudawa gami da munafukai daga cikin musulmi masu kae manufofin yahudawa domin rusa al’ummar musulmi suke kitsawa.

Daga cikin kuwa har haifar da wasu kungiyoyi masu dauke da akidar wahabiyanci da suke aikata ayyukan ta’addancia duniya domin bata fuskar musluncia idon duniya, baya ga haka kuma suna kasha makudan kudade domin yada rarraba a tsakanin musulmi da sunan banbancin mazhaba, wanda kuma hakan ne yasa muusulmia kasashe da dama sun manta da makiyansu an asali sun koma fada da junans da kafirta junansu saboda sabanin ra’ayi, wanda kuma kuma ba shi ne tushe addini ba.

Ya ce hakiak za a iya cewa a wannan bangare makiya ta hanyar yin amfani da munafukan shugabannin da sarakuna na wasu kasashen musulmi, sun samu nasara wajen raunana musulmi, domin kuwa a halin yanz musulmi sun manta da makiyansu na asali sun koma kallon junas a matsayin makiya.

Irin wannan mummunan aiki da munafukan musulmi suka yi wa Amurka da yahudawa, ya kara nisantar da wannan al’umma ta amnzon Allah daga koyarsawa, ya kara nisatar da wannan al’umma ta musulmi daga hadin kai da manzon Allah ya dora ta a kansa, ya nisantar da ita daga sunnarsa mai tsarki, inda aka koma bin Amurka da yahudawa da aiwatar da manufofinsu da sunan sunnarsa.

3667975


captcha