IQNA

21:41 - December 10, 2017
Lambar Labari: 3482187
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taro na kasa da kasa  akan sirar manzon Allah (SAW) a birnin Nuwakshaut na kasar Mauritania.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aqlame.com cewa, ana shirin gudanar da zaman taro na kasa da kasa  akan sirar manzon Allah (SAW) a birnin Nuwakshaut na kasar Mauritania fadar mulkin kasar.

Wannan taro zai samu halartar masana daga kasha 20 na duniya, inda za a gabatar da bayanai da kuma kasidu kan tarihin manzon Allah da kuma muhimman lamurra da ya kamata a mayar da hankalia  akansu dangane da tarihinsa da rayuwarsa mai albarka.

Daga cikin kasashen da za su ahalartar na larabawa da kuma wasu daga cikin nahiyar Afirka da kuma yankin Asia gami da gabas ta tsakiya.

3671167

 

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: