IQNA

Wani Kirista Ya Samu Shedar Karatu Ta Dakta A kan Shari’ar Musulunci

23:53 - December 18, 2017
Lambar Labari: 3482212
Bangaren kasa da kasa, Nabil Luka Babwi wani kirista ne a kasar Masar wanda ya samu shedar karatu a bangaren shari’ar musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, Nabil Luka Babwi kirista a kasar Masar wanda ya samu shedar karatu a bangaren shari’ar musulunci ta dakta.

A tattaunawarsa da tashar talabijin ta Alhadas ya bayyana cewa, ya gudanar da bincike mai zurfi a kan kur’ani da sunna, kuma ya yi rubutunsa  a kan hakan, da kuma irin gudunmawar da kiristoci za su bayarwa a cikin kasashen musulmi.

Ya ce ko shakka babu abin da ya iya ganowa a cikin tsawon shekarun da ya kwashe yana binci kan addinin muslunci a cikin ku’ani da sunna shi ne, musulmi da kiristoci sun hadu a kan abubuwa kusan casein da tara cikin dari, inda suka samu abani bai wuce kasi daya cikin dari ba, shi ma yana da alaka da akida ne.

Dangane da irin gudunmawar da kiristoci za su baya a cikin kasashen musulmi kuwa, ya bayyana cewa hakika musulmi da kiristoci suna da kusanci, saboda haka dole ne dukkanin bangarorin biyu su rungumi juna.

3673778

 

 

 

 

captcha