IQNA

Jami'an 'Yan Sanda Sun Kai A Wata Makaranta A Mombasa Kenya

23:55 - December 20, 2017
Lambar Labari: 3482220
Bangaren kasa da kasa, jami'an 'yan sanda sun kaddamar da farmaki a kan wata makaranta a yankin Mombasa da sunan yaki da ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a jiya jami'an 'yan sanda sun kaddamar da farmaki a kan wata makaranta a yankin Mombasa da sunan yaki da ta'addanci tare da kame wasu daga dalibai da malaman makarantar.

Rahoton ya ce tun kafin wannan lokacin dai jami'an tsaro sun jima suna sanya ido a kan wannan makarantar da dukkanin ayyukan da ake gudanarwa a wurin, bisa zargin cewa ana yin wasu abubuwan da suka yi kama da koyar da ta'addanci.

Jami'an tsaro dai sun yi awon gaba da dalibai kimanin 100 da kuma malamai 4, inda suke ci gaba da rike su da sunan gudanar da bincike kan zargin da ake.

Wani jami'in 'yan sanda a yankin ya sheda cewa, sun dauki wannan matakin ne sakamakon wasu rahotannin sirri da suka samu da ke tabbatar musu da cewa akwai lamun wasu aikace-aikace da suka yi kama da lamurran 'yan ta'adda da suke wakana a wurin.

Ya kara da cewa yanzu dukkanin dalibai da malaman da suka kama suna yi musu tambayoyi ne, kuma da zaran sun gama za su sale su domin su koma gidajensu.

Babu wata alama da 'yan sandan suka a wannan makaranta da ke nuni da cewa ana aikata wani abu na koyar da ta'addanci, kamar yadda dukkanin mutane yankin sun bayar da sheda kan cewa babu gaskiya kan zargin da 'yan sanda suke yi.

3674584

 

captcha