IQNA

A Cikin Sakon Shugaban Kasa Na Sabuwar shekara:

Ina Fatan Shekara Ta 2018 Ta Zama Shekarar Farin Ciki Da Zaman Lafiya A Duniya

23:42 - December 25, 2017
Lambar Labari: 3482233
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Iran ya taya mabiya addinin Kirista murnar tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa dan Maryam {a.s} da ma dukkanin mabiya addinai da suka zo daga wajen Allah Madaukaki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A sakonsa na taya mabiya addinin kirista murnar tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa a yayin zaman taron ministocin kasar Iran a jiya Lahadi: Shugaban kasar Dr Hasan Ruhani ya bayyana cewa; Bikin tunawa da haihuwar Annabi Isa ba kawai lamari ne da ya shafi mabiya addinin Kirista ba, domin ya shafi al'ummar musulmi da ma sauran al'ummu, don haka yana taya dukkanin al'umma murnar tunawa da zagayowar wannan rana mai albarka da fatan shiga shekara ta 2018 cikin koshin lafiya da alkhairi.

Dr Ruhani ya kara da cewa: Tunawa da ranar haihuwar Annabi Isa tunawa ce da saukar sakon shiriya da Annabi Isa ya zo da shi da nufin shiryar da al'umma zuwa ga kadaita Allah da yin riko da kyawawan dabi'u gami da wanzar da zaman lafiya da soyayya a kan doron kasa.

3675881

 

captcha