IQNA

An Dakile Harin Boko Haram A Maiduguri

23:50 - December 26, 2017
Lambar Labari: 3482239
Bangaren kasa da kasa, Rundunar sojin Najeriya sun sanar da dakile wani harin ta'addanci da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi yunkurin kai wa a birnin Maiduguri a ranar Kirsimeti.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto cewa, an ji karar musayar wuta tsakanin mayakan na Boko Haram da dakarun sojin Najeriyar daga kauyen na Molai mai nisan kilomita biyar daga cikin garin Maiduguri. to sai dai kakakin Sojin da ke Maiduguri ya bayyana cewa sun dakile harin.

A baya-bayan nan dai Mayakan na Boko Haram sun dawo da kai hare-hare sassan kasar musamman yankin arewa maso gabashin kasar  inda a nan ne ayyukansu ya fi tsananta,

Duk da cewar ba a samu asarar rai ba bisa nasarar da aka samu kan mayakan, an karfafa matakan tsaro a duk fadin yankin da ya sha fama da ayyukan kungiyar.

 Fiye da mutane  miliyan biyu rikicin Boko Haram din ya raba da mahalinsu, bayan wasu duban mutanen da suka rasa rayukansu. 

3676457

 

 

 

captcha