IQNA

Gasar Kur'ani Ta Kasa A Najeriya A Wata Mai Zuwa

16:38 - December 27, 2017
Lambar Labari: 3482240
Bangaren kasa da kasa, a cikin wata mai kamawa ne za a gudanar da gasar kur'ani ta kasa a Najeriya karo na 32 tare da halartar wakilai daga sassan kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin New Teleghraph cewa, gasar za a gudanar da ita ne a garin Katsina da ke arewacin kasar tare da halartar makaranta da mahardata.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan gasa za a gudanar da ita ne a karo na talatin da biyu, inda za ta kunshi bangarorin hardar hizib 10 da kuma na 20, sa kuma 40, da kuma dukkanin kur'ani a dukkanin bangarori na tilawa da kuma harda.

Babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce jan hankulan matasa domin komawa zuwa ga lamarin kur'ani mai tsarki, tare da mayar da hankali yadda ya kamata.

Tun a cikin shekara ta 1986 ce aka fara gudanar da irin wannan gasa ta kasa baki daya a Najeriya, inda akan samu halartar wakilai daga dukkanin jahohin kasar, musamman ma wadanda musulmi suka fi rinjaye a cikinsu.

Najeriya dai tana da yawan mazauna da suka haura miliyan 186, kuma ita kasar Afirka mafi girma ta fuskar yawan jama'a da kuma yawan man fetur.

3676811

 

 

 

 

captcha