Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Qatari Alarab ta bayar da rahoton cewa, a cikin wanann sabuwar shekara za a gudanar da gasar kur'ani ta kasa mai taken idin kur'ani a kasar Qatar karo na bakawai.
Bayanin ya ce bababr manufar gudanar da wannan gasa wadda za ta kebanci 'yan kasar Qatar zalla ita ce kara karfafa harkokin da suka shafi kur'ani mai tsarki a cikin gida, musamman ma a tsakanin matasa.
Gasar dai za ta hada da bangarorin karatu da kuma harda, kamar yadda bangaren hardar zai takaitu da gajerun surori ne kawai.
Kasar Qatar a cikin shekarun baya-bayan nan ta himmatu wajen shirya taruka da suka shafi kur'ani a cikin gida, kamar yadda kuma ta shirya tarukan kasa da kasa na kur'ani tare da halartar baki daga kasashen duniya.
Daga karshe za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo a cikin wannan gasa da za a gudanar.
Malamai da limaman masallatai dai basu daga cikin wadanda za su shiga wannan gasar, inda lamarin zai takaitu ga sauran jama'ar gari musamman ma matasa.