IQNA

Daliban Kur’ani 7000 Ne e Karatun Allo A Wahran

23:52 - January 04, 2018
Lambar Labari: 3482266
Bangaren kasa da kasa, daliban kur’ani kimanin 7000 ne suke yin karatun allo makarantu daban-daban a garin wahra na kasar Ajeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-massa.com cewa, bisa kididdiga da aka yi daliban kur’ani kimanin 7000 ne suke yin karatun allo makarantu daban-daban a garin wahra na kasar Ajeriya tare da amincewar mahaifansu.

Daga cikin wadannan dalibai 7000, wasu kimanin 4500 sun yi nisa a cikin karatunsu, yayin da wasu kimanin 2500 har yanzu suna a matakin farko ne.

Bayanin ya ci gaba da cewa mafi yawan daliban makarantun allo a wannan gari ‘yan mata ne, kuma akwai malami kimanin 420 da suke koyar da su don kashin kansu.

Ma’aiatar kula da harkokin addini ta kasar ta dauki wasu sabbin matakai na taimaka ma makarantun allo ta hanyoyi daan-daban.

Daga cikin hanyoyin har da aikewa da malamai da za su taimaka ma malaman da sabbin hanyoyi na koyarwa domin samun sauki, da kuma bayar da taimako na kudade da kayyakin bukata domin koyarwa.

3678787

 

 

 

 

 

captcha