IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta ‘Yan Kasashen Ketare A UAE

22:11 - January 05, 2018
Lambar Labari: 3482269
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki wadda ta kebanci ‘yan kasashen waje mazauna kasar hadadiyar daular larabawa a Ra’asul Khaimah.

Kafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Ittihad cewa, a halin yanzu an fara gudanar da gasar ne a bangaren maza, inda za a dauki tsawon kwanai ana gudanar da ita.

A ranar Talata mai zuwa kuma za a fara gudanar ad gasar a bangaren mata, inda za a dauki tsawon kwanaki uku a wannan bangaren na gasar.

Ahmad brahim Sabian shi ne babban darakta na kwamitin gasar kur’ani a kasar haddadiyar daular larabawa, ya bayyana cewa wannan gasa ana gudanar da ita a karo na goma sha tawas, kuma komai yana tafiya cikin nasara kamar yadda aka tsara tare da dukkanin dauki da goyon bayan daga sarkin Ra’asul Khama Sheikh Saud Saqar Kasimi.

Abdulrahman Mijdad shi ne mataimakin shugaban kwamitin gasar kur’ani na hadaddiyar daular arabawa, ya bayyana cewa wannan gasa tana samun halartar masu su gasa su 763 da mata, kuma daga karshe bayan kammala gasar akwai kayutuka da za a ayar ga dukkanin mahalarta gasar, sai kuma yautuka na musamman ga dukkanin wadanda suka suka nuna kwazo.

3679213

 

 

 

 

captcha