IQNA

Kungiyar Jihadul Islami Ta Kirayi Jerin Gwanon Juma’ar Nuna Fushi

22:20 - January 05, 2018
Lambar Labari: 3482271
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Jihadul sami ta kirayi jerin gwanon juma’ar nuna fushi da kuma kare masallacin Quds a yau.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin bayanin da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa tana kira ga dukkanin al’umma mazauna zirin gaza da su fit yau a yankin Khan Yunus domin gudanar da gagarumar zanga-zanga a yankin domin yin Allah wadai da kudirin mayar da birnin Quds na yahudawa.

Bayanin ya ce wannan yana a matsayin martani ne na al’ummar Palastinu kana bin da gwamnatin Amurka da kuma yahudawan sahyuniya suke yin a tauye hakkokin al’ummar Palastin, musamman ma hakkinsu na birnin Quds.

Tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da amincewa da birnin Quds a matsayin babban birnin Isra’ila a hukumance, al’ummomin musulmi da na duniya suke ci gab ada yin Allah wadai da hakan.

3679224

 

 

captcha