IQNA

Kyamar 'Yan Sanda Musulmi A Birnin New York

16:53 - January 09, 2018
Lambar Labari: 3482283
Bangaren kasa da kasa, majiyoyin rundunar 'yan sanda a birnin Newr ta bayar da rahoton cewa, an kai ci zarafin wasu 'yan sanda musulmi a yankin Bronx.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga nydailynews cewa, majiyoyin rundunar 'yan sanda a birnin Newr ta bayar da rahoton cewa, an kai ci zarafin wasu 'yan sanda musulmi a yankin Bronx a lokacin da sukea  kan aikinsu.

Wannan lamari dai ya zo a lokacin da wadannan 'yansantda suke suke gudanar da ayyukansu a kan titi, inda wasu masu wucewa da suka fahimci cewa muuslmi ne, suka ci zarafinsu tare da yi musu kalamai na batunci.

A shekarar da ta gabata ce babban jami'in 'yan sanda na birnin New York ya bayar da bayanin cewa, an fara samun kyamar 'yan sanda msuulmi a birnin ne tun bayan da Trump ya dare kan kujerar shugabancin Amurka.

Yanzu haka dai akwai 'yan sanda fiye da dubu daya da suke aiki a cikin rundunar 'yan sanda ta New York.

3680391

 

 

 

 

captcha