IQNA

Jagoran Juyin Muslunci A Wurin Darasi:

Amurka Ta Mayar Da Daesh Zuwa Afghanistan Ne Domin Ta Ci Gaba Da Zama A Yankin

16:41 - January 30, 2018
Lambar Labari: 3482349
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran a lokacin da yake shiri fara bayar da karatu na bahsul kharij a yau Talata ya bayyana cewa hankoron Amurka na mayar da Daesh cikin Afghanistan da cewa, hakan hanya ce ta neman ci gaba da zama a cikin yankin.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, bayan ya isar da ta'aziyyarsa ga mutanen kasar Afghanistan kan hare-haren ta'addancin da ya lashe rayukan mutane da dama a cikin kwanakin nan, ya ce Amurka ce take karfafa yan Taliban a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran ya bayyana haka ne a safiyar yau Talata, ya kuma kara da cewa tun lokacin da aka sami nasarar korar  kungiyar yan ta'adda ta Daesh daga kasashen Iraqi da Syria Amurka ta fara daukar su daga gabas ta tsakiya zuwa kudancin Asia, don halasta samuwarta a yankin.

Jagoran ya kara da cewa gwanatin kasar Amurka ta mamaye kasar Afghanistan tun shekara ta dubu biyu da daya, wato shekaru sha bakwai da suka gabata, da sunan yaki da kungiyar qaeda, amma tun lokaci mutanen kasar ba su sake samun zaman lafiya ba. 

Dubban mutanen Afghanistan ne suka rasa rayukansu a cikin yan watannin da suka gabata sanadiyyar hare-haren kungiyar Daesh da kuma Taliban, wadanda dukkaninsu Amurka ce ta samar da su.

3686681

 

captcha