Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na cibiyar yada al'adun musulunci ya habarta cewa, wannan festival za a gudanar da shi ne domin tunawa da cikar shekaru 39 da samun nasarar juyin juya halin muslunci a Iran.
Bayanin ya ci gaba da cewa,a kowace shekara ofishin jakadancin kasar Iran kan dauki nauyin shirya irin wadannan taruka akasashen duniya daban-daban, da hakan ya hada har da kasar Kenya.
Daa muhimman abubuwan da za a gudanar da nuna fim din Maryam Muqaddas wanda aka shirya akasar, wanda yake bayyana tarihin sayyida Marya mahaifiyar annabi Isa amincin Allah ya tabbata a gare shi a mahangar addinin muslunci kamar yadda ya zo a a cikin kur'ani.
Za a nuan fim din ne tare da halartar daliban jami'a da kuma malamain jami'ioi gami da jami'an huldar diplomasiyya na kasashen duniya da suke a kasar ta Kenya.
A gefe guda kuma akwai baje kolin kayayyakin fasaha da suka hada da zane-zanen da ayyukan hannu na kasar Iran.