IQNA

Bayani Kan Gasar Kur'ani Ta Makafi Ta Duniya

21:00 - February 05, 2018
Lambar Labari: 3482366
Bangaren gasar Kur'ani, za a gudanar da gasar kur'ani ta makafai ta duniya karo na uku kamar yadda aka saba gudanarwa a shekarun da suka gabata.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, gasar za ta fara ne daga ranar 30 ga Farvardin zuwa 6 ga watan Ordibehesht shekarar 97 ta shamsiyya.

Kamar yadda gasar ta gudana a shekarar da ta gabata,a bana ma mutum zai zo bayan cika sharudda, tare da dan rakiya, kamar yadda kuma adadin mutane da za su daga kasa, to dan rakiya guda ne.

Kuma wadanda za su shiga gasar shekarunsu sun kama daga 18 ne zuwa 45, kuam hukumar kula da gasar kur'ani ta kasar a jamhuriyar muslunci za ta dauki nauyinsu, bisa sharadin su zama sun iya karatun kur'ani tare da kiyaye kaidoji da hukunce-hukuncensa, gami da kyakyawar muryar karatu.

Abin da ake bukata shi ne kwafin fasfo da kuma kanan hotuna guda biyu, hade da fam da aka tura ma mutum na rijista, kuma ranar karshe ita ce 16 ga Isfand 1396, 18 ga Jumada thani 1439, wato 7 ga watan Maris 2018.

Shafin yanzr gizo na gasar www.quraniran.ir da kuma wayar tarho: 00989223784093 da kuma Fax 00982164872627 sai adireshin email; awqafiran@yahoo.com za a iya yin amfani da wannan lamba domin shiga whatsapp ko telegram: 00989223784093.

Domin tuntuba a cikin harsunan Farisanci, turanci da Larabci sai a matsa nan (click) domin samun bayani.

3683142

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha