IQNA

Wani Makaranci Mai Larura Ya Kai Mataki Na Karshe A Gasar Ra’asul Khaimah

21:05 - February 05, 2018
Lambar Labari: 3482367
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Nasr Ahmad wani matashi ne mai shekaru 18 da ke fama da larura wada ya kai ga mataki na karshe a gasar kur’ani ta Raasul Khaimah.

Kamfanin dillancin labaran qna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-imarat yaum cewa, Muhammad Nasr Ahmad wani matashi ne mai fama da larura ta karancin gani da kuma rashin girman jiki, wada ya kai ga mataki na karshe a gasar kur’ani ta Raasul Khaimah a kasar hadaddiyar daular larabawa.

Ya fara karatun kur’ani mai tsarki ne ne a matsayin harda tun yana da shekaru 9 a duniya, inda yakan halarci wata cibiyar karatun kur’ani mai tsarki, daga nan yake saurare yana hardacewa.

Kasantuwar yana da matsalar karancin gani, hakan ya sanya sai dai ya ika sauraren karatun yana maimaitawa har ya hardace, kamar yadda kuma abokansa suna karanta masa ayoyin kur’ani yana sarare, daga nan kuma yana maimaitawa.

Yanzu haka dai Nasr yana a makarantar sakandare ne, amma kuma yana samun ci gaba matuka a karantunsa, duk kuwa da larurar da yae fama da ita a jikinsa.

Kamar yadda kuma yanzu ya hardace izihi arbain da shida, kuma yana ci gaba da kokari domin ganin ya kammala hardar kur’ani baki daya.

A gasar karatuRa’ da hardar kur’ani da ake yi a Ra’asul Khaima, ya samu wuce matakan share fage da kuam matakan fako da na tsakiya, inda yanzu ya kai ga matakin karshe.

A matakin farko gasar mutane 1550 ne, amma ya zuwa yanzu mutae 357 ne suka yi saura.

3688612

 

captcha