IQNA

Babban Malamin Kasar Libya Ya Kira Mahukuntan Saudiyya ‘Yan Kama Karya

22:52 - February 07, 2018
Lambar Labari: 3482375
Bangaren kasa da kasa, Sadiq Garyani babban malamin addini mai bayar da fatawa a kasar Libya ya caccaki mahukuntan kasar Saudiyya tare da bayyana sua  matsayin ‘yan kama karya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Aljazeera cewa, babban malamin na Libya ya bayyana cewa, mahukuntan masarautar Al Saud suna yin amfani da mulkinsu wajen muzgunawa jama’a da cin zarafinsu.

Ya ce yanzu haka akwai dubban mutane a cikin gidajen kason Al Saud, da suka hada da malaman addini da masana da masu kare hakkokin bil adama da kuma masu fafutuka da ‘yan siyasa, mafi yawa daga cikinsu ana tsare ne da su bisa zalunci.

Dangane da matsayin abin da mahukuntan Al saud suke yi da sunan addini, ya bayyana cewa wadannan mutane da suke rke da madafun iko a kasa mai tsarki gurbatattun mutane ne da suke cutar da musulmi da addinin musulunci.

A daya bangaren kuma ya bayyana cewa yanzu haka akwai wasu daga malaman kasar Libya da suka tafi aiki umra da Al Saud suka kame su, kuma har yanzu ba a san makomarsu ba, kamar yadda har yanzu Al saud sun ki su ce uffan kan batun.

3689413   

 

captcha