IQNA

Kungiyoyin Karen Hakkin Bil Adama Sun Yi Allawadai Da Hare-Haren Libya

18:52 - February 10, 2018
Lambar Labari: 3482384
Bangaren kasa da kasa, kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun yi Allah wadai da kakakusar murya dangane da hare-haren ta'addancin da aka kai Libya wanda ya lashe rayukan mutane 86.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alfajr cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun yi Allah wadai da kakakusar murya dangane da hare-haren ta'addancin da aka kai a wani masallaci a Benghazi Libya da bama-bamai,  wanda ya lashe rayukan mutane da dama.

Bayanin ya ce hakika mutanen da suke aiwatar da wannan basu da wata alaka da duk wata akida ta addini ko wani tunani na 'yan adamtaka, domin kuwa hakan ya tabbatar da dabbancin da ke tattare da su.

Bayan kai harin nan jiya a nan take mutane 75 ne suka rasa rayukansu wasu da dama kuma suka jikkata, amma daga bisani adadin wadanda suka mutu ya ci gaba da karuwa.

A yau kuma wasu rahotannin sun ce an kaddamar wasu hare-haren da a yankin Tisin da ke cikin gungimar Sirte inda  anan ma aka kashe mutane da dama.

Mahukuntan Libya suna zargin wasu kasashen larabawa masu yada  akidar tsatsauran ra'ayin da hannu a dukkanin ayyukan ta'addancin da irin wadanda kungiyoyi suke aikatawa.

Kungiyar kare hakkokin larabawa wadda aka kafa a cikin shekara ta 2000 tana daga cikin wadanda suka yi Allah wadai da harin, wadda ta hada kasashe 16 na larabawa.

3690352

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha