Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na alyaum24.com cewa, Nasir Qasabi dan wasan kwaikwayo na Saudiyya dangane da wani furuci da ya yi kan shafinsa na twitter kan uhimmancin karatun kur’ani an samu ra’ayoyi mambantaa tsakanin masu binsa shafinsa.
A cikin shafin nasa ya rubuta cewa; karatun kur’ani mai tsarki yana bude muryar mutum ta yi kyau sosai, sannan kuma yana kara ma mutum fasahar magana.
Wannan furuci ya fusata wasu, inda suke ganin cewa danganta kur’ani da batun kyawun sauti musamman gare su ‘yan wasan kwaikwayo, hakan cin zarafin kur’ani ne, yayin da kuma wasu suke ganin hakan a matsayin magana mai kyau.
Ya ce tun suna dalibai a jami’a wani malaminsu yana gaya musu cewa, su rika karanta kur’ani za su samu fasahar magana, kuma ya ga hakan a aikace.