IQNA

Gasar Kur'ani Ta Masu Nakasa Da Bukatu Na Musamman A Masar

20:53 - March 03, 2018
Lambar Labari: 3482448
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta nakasassu da kuma masu bukata ta musamman a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa, za ta shirya gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta nakasassu da kuma masu bukata ta musamman.

Wannan gasa dai za ta kunshi matasa 'yan kasa da shekaru 25 daga dukaknin sassan kasar.

Haka nan kuma gasar  zata mayar da hankali a bangaren harda daga juzui na 15, haka nan akwai juzui na 28, 29, 30, amma wannan bangaren zai shafi kalmomi ne da bayanin ma'anoninsu.

Sharadin gasar dais hi ne wadanda za su halarta shekarunsa kada su wuce ashirin da biyar, kuma ba su halarci wadanda aka gudanar a cikins hekaru biyar da suka gabata ba.

Daga karshe za a bayar da kyautuka ga wadanda suka fi nuna kwazoa  gasar.

3696097

 

captcha