Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun musulunci cewa, wannan yana daga cikin manyan tarukan da aka sabagudanawa a kasar.
Bayan bude taon da taken kasa ta Senegal, suhgaban karamin ofishin jakadancin Iran a Senegal Sayyid Hassan Esmati ya gabatar da karatun kur’ani mai tsarki.
Bayan nan kuma n ci gaba da gudanar da taron, inda ‘yan makaranta daga dukkanin bangarori na kasar suka halarta, kuma an farati na girmama wag a kr’an da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.
Mutane da dama ne suke haartar taron, inda shugaban kasa Maky Sall da kansa da wasu daga ministoci da manyan daraktoci sun halarci wannan taro.
Su a nasu bangaren manyan malaman addini na kasar gami da limamai duk sun halarta, inda aka bayar da damar gabatar da jawabai daga wasu malamai, da kuma wasu jami’an difomasiyya na kasashen muuslmi, daga ciki har da karamin jakadan Iran a kasar.