Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar quds Alarabi cewa, Hana Isa babban sakataren cibiyar hadin kan musulmi da kiristoci a Palastinu ya bayyana cewa, Isra'ila ta kafa wasu sabbin dokoki da nufin kwace kaddarorin da majami'oin mabiya addinin kirista suka mallaka, musamman tsohon birnin Quds.
Ya ce dokar ta bukaci kimanin dalar Amurka miliyan 191 daga majami'oin domin barin kaddarorinsu a hannunsu, idan kuma ba haka gwamnatin yahudawa za ta kwace wadannan kaddarori, wadanda suka hada da makarantu, asibitoci, filaye, da sauransu, kuma an kafa wannan dokar ne bisa masaniyar cewa majami'ioin ba za su iya biyan wadannan kudade a matsayin haraji ba.
Kimanin kashi 28 na kaddarorin majami'oin kiristoci a Palastinu suna cikin yankin tsohon birnin Quds ne.
Hana Isa ya ce majami'oin mabiya addinin kirista ba za su biya wadannan kudaden haraji da Isra'ila ta kakaba musu ba, domin hakan baya a kan doka.