Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an kammala aikin gyaran masallacin cibiyar Azhar bayan gyara na tsawon shekaru uku a jere, za a bude masallacin ne tare da halartar dan gidan sarkin Saudiyya yarima mai jiran gado, da shugaban Masar Abdulfattah Sisi, da babban malamin Azhar Ahamd Tayyib.
An yi amfani da fasaha ta zamani wajen gyaran masallacin, inda aka wasu nauoin duwatsu wajen shimfida dabensa, haka nan an saka tagogi masu sarrafa kansu, gam da tsarin kasha gobara mai sarrafa kansa.
Duk wannan aiki an gudanar ad shi tare da kiyaye muhimman abubuwa na tarihi da sukea wannan masallaci, ba tare da an taba su ko sauya musu wurare ba.