IQNA

Zaman Kungiyar Kasashen Larabawa Kan Harin Isra’ila A Gaza

23:50 - April 01, 2018
Lambar Labari: 3482531
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar kasashen larabawa za ta gudanar da zaman gaggawa dangane da kisan gillar da Isra’ila ta yi wa Palastinawa 17 a yankin Zirin Gaza.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wata majiyar diflomasiyya a kasar Jordan ta tabbatar da cewa, za a gudanar da zaman nea  matsayi na wakilan kasashen larabawa a kungiyar, domin daukar matakai na nuna kin amincewa da wannan danyen aiki da Isra’ila take aikatawa kan al’ummar Palastine.

Rahoton ya kara da cewa, ana sa ran wannan zama zai gudana a yau Lahadi ko kuma a gobe Litinin, kamar dai yadda bangaren Palastinawan suka nemi da a gudanar da zaman.

A wannan zaman dai kasashen larabawan za su bayyana matsayinsu na yin Allah wadai da hare-haren Isra’ila kan yankin Gaza da kuma kisan palastinawa da ta yi a ranar Juma’a a lokacin da suke yin gangamin ranar kasa.

A jiya ma kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kasa fitar da wani kudiri na yin Allah wadai da wannan kisan gilla da Isra’ila ta yi Palastinawa, kwamitin ya kasa daukar matakin saboda Amurka taki amincewa da hakan.

3702546

 

 

 

 

captcha