Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da wani baje kolin hijabin musulunci dinkin kasar Iran a jami’ar muslunci ta kasar Ghana wanda ya samu halartar masu sha’awar hijabin musulunci.
Mohsen Ma’arifi shi ne shugaban jami’ar musulunci ta kasar Ghana kuma wakilin jami’ar Almustafa (SAW) a kasar, ya gabatar da jawabi a yayin bude baje kolin.
A cikin jawabin nasa ya bayyana cewa, akwai hikima a cikin umarnin uabngiji na sanya mata suka hijabi, domin kuwa yin hakan da farko yana a matsayin kariya ga mutuncin mace, kamar yadda hakan kuma yana da bababn tasirin wajen tarbiya a zamantakewar jama’a, wanda yana rage yawan barna ta fuskar mu’amala ta haram tsakanin mata da maza.
Haka nan kuma ya bayyana cewa baya ga haka kuma, a hakikanin gaskiya hijabi shi ne ado ga mace ba tsiraici ba.
Bayan jawabin nasa wakiliyar ma’aikatar kula da harkokin mata da kanan yara ta gabatar da nata jawabin, inda ta yaba matuka da himmar da jami’ar musulunci take da ita wajen wayar da kan jama’a, da kuma karfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma.