Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yanar gizo na Watan ya habarta cewa, mas’ud Ganayim wani dan majalisar dokokin Isra’ila mai wakiltar larabawa, ya rubuta wata wasika zuwa ga ministan harkokin kasuwanci na Isra’ila tare da jan hankalinsa kan ya sake shawara dangane da aniyarsa ta mayar da masallacin tarihi zuwa kasuwa.
A cikin wasikar tasa zuwa ga ministan harkokin kaswanci na haramtacciyar kasar Ira’ila Masud Ganayim ya bayyana cewa, wannan wuri na al’ummar muuslmi ne, wanda Isra’ila bata da hakkin taba shi, kuma daukar duk wani mataki na taba wannan masallaci zai fuskanci fushi daga al’ummar musulmi.
Tun ‘yan shekarun da suka gabata ne yahudawa masu satsauran ra’ayi suka kwace iko da wanann masallaci, daga bisani kuma suka mayar da shi wurin zubar da shara.
An gina wannan masallaci nea tun a cikin shekara tun a karni na 18 na shekarar miladiyya a yankin tabriyya.